Najeriya

Najeriya zata binciki zargin cin zarafin dan adam da ake wa sojinta

Babban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai.
Babban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai. AFP PHOTO/STRINGER

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana shirin ta na gudanar da bincike kan cin zarafin dan’adam da ake zargin wasu daga cikin jami’anta dake yaki da kungiyar Boko Haram sun yi.

Talla

Shugaban rundunar sojin Janar Tukur Yusuf Burutai ne ya bayyana haka, a lokacin da yake kaddamar da wani kwamiti na musamman da yace zai duba zarge zargen da suka kunshi wadanda suka fito daga kungiyar Amnesty International da kuma na masu fafutukar kafa kasar Biafra.

Yayin zantawarsa da RFI hausa Janar Sani Usman Kukasheka, Daraktan yada labaran rundunar ya ce, a ko da yaushe dama rundunar sojin Najeriya, a shirye take ta magance matsalar cin zarafin dan’adam daga sojin Najeriya.

A cewar Janar Usman rundunar sojin Najeriya nada kyakkyawar alaka da kungiyoyin kare hakkin dan’adam.

Najeriya zata binciki zargin cin zarafin dan adam da ake wa sojinta

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI