Najeriya

Wasikar yan Majalisun Najeriya zuwa Shugaban Kwastam

Kanal Hamid Ali (rtd) Shugaban Kwastam a Najeriya
Kanal Hamid Ali (rtd) Shugaban Kwastam a Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban hukumar kwastam na kasar Hamid Ali da ya bayyana a gabanta a ranar laraba ta makon gobe, bayan da hukumar ta kwastam ta ce ba ta da niyar ja da baya a game da yunkurin gudanar da binciken kwakwaf akan motoci domin tabbatar da cewa sun shigo kasar ne akan ka’ida.

Talla

Majalisar dattawan ta bukaci Hamid Ali ya gurfana gabanta a ranar ta laraba, sannan kuma dole ne ya kasance sanye da kakin irin na kwastam .

Idan aka yi tuni yan Najeriya sun soma mayar da martani da kalamai masu zafi kan umurnin shugaban hukumar kwastam Hameed Ali na kwace duk wata mota da aka shiga da ita kasar daga ranar 2 ga watan gobe, muddin aka gano cewar bata biya harajin gwamnati ba ko kuma tana dauke da takardu na bogi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.