Najeriya

INEC ta sanar da ranar zaben 2019 a Najeriya

Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu

Hukumar Zaben Najeriya INEC, ta sanya ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2019 a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa da na 'Yan Majalisun Tarayya.

Talla

Sanarwar da hukumar ta fitar ta nuna cewar za a gudanar da zaben Gwamnoni da na 'Yan Majalisun Jihohi a ranar 2 ga watan Maris.

Hukumar ta kuma sanar da cewar ta dora jami’an ta 23 da ake tuhuma a kotu da laifin magudin zabe kan rabin albashi har sai an kammala shari’ar da ake yi musu.

INEC ta dai bai wa ‘yan Najeriya tabbacin gudanar da zaben cikin tsari tare da daukan mataki kan duk wani jami’inta da aka samu da aikata laifin karya dokokin zabe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.