A shirye na ke na sasanta da Kwankwaso- Ganduje
Wallafawa ranar:
Masu sa ido a siyasar Kano da ke Najeriya sun bayyana cewar, rashin jituwar da ta fito fili tsakanin Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje da tsohon mai gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na yi wa jihar tarnaki wajen ci gaban da aka dauko.
Sai dai Gwamna Ganduje ya ce a shirye yake ya sasanta da Sanata Kwankwaso don ganin an dinke barakar da ke tsakaninsu.
A zantawarsa da RFI hausa, Gwamnan ya ce, akwai ‘yan ziga a rashin jituwar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan na Kano.
Ga dai abinda Gwamna Ganduje ke cewa a hirarsa da wakilinmu na Kano Abubakar Isa Dandago.
A shirye na ke na sasanta da Kwankwaso- Ganduje
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu