Najeriiya

Shugaba Buhari na Najeriya ya koma gida

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gida daga birnin London, in da ya shafe tsawon kwanaki 49 yana jinya, abin da ya haifar da cecekuce a dukkanin fadin kasar. 

Lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a filin tashi da saukan jiragen sama na barikin sojin kasar da ke jihar Kaduna
Lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a filin tashi da saukan jiragen sama na barikin sojin kasar da ke jihar Kaduna RFI Hausa/Sadou
Talla

Jirgin shugaba Buhari ya  sauka ne a filin tashi da saukan jiragen sama na barikin sojin sama da ke jihar Kaduna da misalin karfe 7 da minti 56, agogon kasar.

Wakilinmu na Kaduna Aminu Sani Sadou da ya ga saukan shugaban, ya ce Buhari ya taka da kansa a filin jirgin, abin da ke nuna cewa ya na cikin koshin lafiya.

Tuni dai wani jirgin sama mai sukan ungulu ya dauke Buhari daga filin jirgin, in da ya nufi birnin tarayya Abuja kamar yadda mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Barnabas Bala Bantex ya shaida wa manema labarai cikinsu har da RFI hausa.

Hoton bidiyon dawowar Buhari

Mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya ce, shugaba Buhari ya gode wa daukacin 'yan kasar da suka yi ta yi masa addu’aoi da fatan alheri.

A ranar 19 ga watan Janairu shugaba Buhari ya tafi hutu a London amma daga bisani aka tsawaita hutun don kammala duba lafiyarsa kamar yadda likitocibnsa suka bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI