‘‘Ba a nada ni don sanya kaki ba’’
Wallafawa ranar:
Shugaban Hukumar Kwastam a Najeriya, Hameed Ali, ya ce ba a bashi wannan mukami domin sanya Kaki ba.
Hameed Ali da ke bayana haka a lokacin wata hira da kafar talabijin TVC da ke Kasar, ya ce kamata ya yi majalisar dokoki ta mayar da hankali kan irin ayyukan da ya ke ba batun sanya kakin kwastam ba.
Majalisar Dokokin Najeriya dai ta bukaci Hammed Ali ya sanya kaki a lokacin da zai halara gabatan don mata bayani kan sabon dokar kudin fito Motocci da hukumar ta bijiro da shi.
Kanar Hameed Ali mai ritaya ya kasance mutum na biyu da ke rike wannan mukami ba tare da taba aikin ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu