Najeriya

'Yan Najeriya sun yanka raguna saboda Buhari

Ministoci da gwamnoni sun taya shugaba Muhammadu Buhari murnar dawowa a fadarsa da ke birnin Abuja
Ministoci da gwamnoni sun taya shugaba Muhammadu Buhari murnar dawowa a fadarsa da ke birnin Abuja Presidential Office/Handout via REUTERS

'Yan Najeriya sun gudanar da bikin murnar dawowar shugaba Muhammadu Buhari daga birnin London, in da ya shafe tsawon kwanaki 49 ya na jinya. 

Talla

Rahotanni sun ce, da dama daga cikin magoya bayan shugaban sun yanka raguna da kaji musamman a jihohin yankin arewacin kasar da suka hada da Katisna da Bauchi da Gombe da Nasarawa da Kuduna da Filato da kuma birnin Tarayya Abuja.

Tuni dai shugaba Buhari ya ce, zai koma bakin aiki a ranar Litinin mai zuwa don ci gaba da jagorancin kasar, yayin da kuma ya mika godiyarsa ga Musulmai da Kirista da suka yi masa adduoin samun lafiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI