Najeriya

An murkushe harin kunar bakin wake a Maiduguri

Jami’an tsaron sun murkushe wani harin bam da wasu mata biyu suka shirya kai wa a garin Maiduguri da ke arewacin Najeriya.

Boko Haram na ci gaba da kokarin kai hare-hare a Borno
Boko Haram na ci gaba da kokarin kai hare-hare a Borno Médecins sans Frontières (MSF) / AFP
Talla

‘Yan kunar bakin wake da basu haura shekaru 18 ba, an gano sune da taimakon ‘yan kato da gora kuma nan take jami’an tsaro suka harbe su kamar yadda kakakin ‘yansanda jihar Victor Isuku ya tabbatar.

A cewar Isuku, ‘yanmata sun shirya kai harin ne cikin gari wanda bai samu ba, kuma babu wanda ya mutu ko ya jikkata face 'yanmata biyu da aka harbe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI