Najeriya

Buhari ya koma bakin aikinsa a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma aiki
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma aiki Presidential Office/Handout via REUTERS

Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya aikewa Majalisar dokokin kasar wasikar dawo wa bakin aiki yau litinni, bayan shafe sama da kwananki 50 baya kasar.

Talla

Mai Magana da yawun shugaban Femi Adesina da ke tabbatar da komawar Buhari aiki, ya ce a wani lokaci yau litinni Buhari zai gana da mataimakinsa kan ayyukan da ya gudanar a bayansa.

A ranar Juma’ar da ta gabata shugaba Buhari ya samu kyakyawan tarba bayan dawowarsa daga London inda ya shafe kusan wata biyu yana jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.