A karshen makon da ya gabata ne aka karrama Gwamnatin Jihar Kebbi a birnin Lagos, saboda gagarumar rawar da manoman ta suka yi wajen noma shinkafa dan ganin kasar ta dogara da kan ta, maimakon sayo shinkafar a kasashen duniya. Bayan bikin, mun tattauna da Gwamnan Jihar Atiku Bagudu kan wannan girmamawa da aka musu, kuma ga abinda ya shaida mana.
Sauran kashi-kashi
-
Bakonmu a Yau Mahamadu Salisu Habi kan rincabewar rikicin Sudan Rikicin sojin da ke ci gaba da faruwa yanzu haka a birnin Khartum na kasar Sudan, na nuna yadda yan siyasar nahiyar Afrika basa daukar darasi, kan abubuawan assha da suka wakana a kasashensu da wasu takwarorinsu dake nahiyar.07/06/2023 04:04
-
Bakonmu a Yau Muhammad Awwal kan yadda ake kamen masu ta'ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya Hukumar yaki da sha da kuma safarar miyagun kwayoyin ta Najerita wato NDLEA na ci gaba da gabatar da mutanen da take kamawa kowanne mako dake safarar kwayoyin ko kuma kokarin fita da su zuwa wasu kasashen duniya.01/06/2023 03:47
-
Bakonmu a Yau Sabuwar gwamnatin Katsina ta sha alwashin magance matsalar tsaro Sabuwar gwamnatin jihar Katsina ta Najeriya da ta yi rantsuwar kama-aiki a wannan Litinin ta bayyana sabbin matakan da za ta dauka wajen magance matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare durkusar da tattalin arzikinta.29/05/2023 03:22
-
Bakonmu a Yau Farfesa Usman Muhammad kan bikin rantsar da sabon shugaban Najeriya A ranar 29 ga watan Mayun 2023, aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya domin maye gurbin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda ya kawo karshen wa’adin mulkinsa na shekaru 8.29/05/2023 03:38
-
Bakonmu a Yau Zainab Ahmed kan basussukan da ake bin Najeriya Yayin da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kawo karshen wa’adin ta a ranar litinin mai zuwa, daya daga cikin zargin da ake mata shine na ciwo basussuka daga hukumomin duniya, wadanda suka yiwa kasar dabaibayi.26/05/2023 03:45