Najeriya

Mutane 46 aka kashe a rikicin kabilanci Ile Ife da ke Najeriya

Mutane 46 aka kashe a Rikicin Kabilancin Ile Ife
Mutane 46 aka kashe a Rikicin Kabilancin Ile Ife ElixirNg

Rahotanni Daga garin Ile Ife da ke Najeriya sun ce mutane 46 aka kashe a fadan kabilancin da aka samu tsakanin Yarbawa da Hausawa.

Talla

Bayanai sun ce, yanzu haka mutane da dama sun tsere sun bar garin dan tsira da rayukansu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike.

Sarkin Hausawa yankin Abubakar Mahmuda Madagali, ya shaidawa RFI Hausa cewa sun tabfka asara dukiyoyinsu.

Abubakar ya kuma ce yanzu haka hausawa sun fara ficewa daga garin domin gujewa aukuwar irin wannan rikici a gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.