Najeriya

Majalisar Najeriya ta sake watsi da nadin Magu

Ibrahim Magu
Ibrahim Magu

Majalisar Dattawan Najeriya ta sake watsi da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzkin kasar ta’annati.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan hukmmar ‘yan san dan ciki ta jaddada matsayinta na cewa, Magu bai cancaci jagorantar hukumar EFCC ba da ke yaki da cin hanci da rashawa.

A cewar Mr. Magu, babu wata gayyata da hukumar SSS ta yi masa don kare kansa game da zarge-zargen da ta ke yi masa, yayin da ya bayyana cewa, ba a yi masa adalci ba.

Sanata Dino Melaye ne dai ya fara tayar da zancen rahoton SSS bayan Magu ya amsa jerin tambayoyi da Majalisar ta yi masa, in da aka zaci cewa yana iya tsallake siradi.

A karo na biyu kenan da Majalisar ke kin tabbatar da Magu bayan akasarin mambobinta sun nuna adawa da tabbatar da shi a yau Laraba.

A cikin watan Janairun daya gabata ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake mika sunan Ibrahim Magu ga Majalisar don tabbatar da nadinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.