Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta tsare jami'anta bisa zargin cin zarafi

Rundunar sojin Najeriya ta ce, tana gudanar da bincike kan wasu jami’anta da ake zargi da cin zarafin wata mata.

Hoton bidiyon wasu jami'an sojin Najeriya yayin da suka ci zarafin wani nakasasshe a Onitsha, da ke jihar Anambra bisa laifin saka kakin soja..
Hoton bidiyon wasu jami'an sojin Najeriya yayin da suka ci zarafin wani nakasasshe a Onitsha, da ke jihar Anambra bisa laifin saka kakin soja.. naijadailies.com
Talla

Rahotanni sun ce matar mai suna Ruth Orji, ta ga ta kanta ce, bayan da sojojin daga bataliya ta 174 dake Ikorodu a jihar Legas, suka lakada mata dukan kawo wuka a ranar Lahadi, sakamakon nuna rashin amincewa da matar ta yi, bisa marin kaninta da wani jami’in soja ya yi.

Bayan aukuwar lamarin ne, aka yada hotunan yadda sojojin suka ci zarafin matar a shafunan internet, abinda da ya sanya mutane da dama, kira da a hukunta jami’an sojin.

Tuni dai rundunar ta sanar da kame jami’an sojin da ake zargi guda 6.

Karo na uku kenan da ake samun aukuwar makamancin haka a cikin wata guda.

Rundunar sojin Najeriya ta nuna rashin jin dadinta bisa aikata cin zarafin da jami’an nata suka yi, tare da godewa ‘yan jaridu bisa rawar da suka taka na fitar da labarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI