Najeriya

Zan cigaba da aiki bisa kishin kasa - Magu

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu. premiumtimesng.com

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Ibrahim Magu, ya ce kin tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar ba zai sauya komai ba dangane da himmarsa ta yaki da cin hanci da rashawa.

Talla

A cewar Magu, babban burinsa, shi ne kakkabe miyagun da ke yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, dan haka zai cigaba da aiki tukuru har zuwa lokacin da wa’adinsa zai kare, ba tare da la’akari da ko an tabbatar da shi ko akasin haka ba, a matsayin shugaban hukumar EFCC.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai majalisar dattawan Najeriya, ta sake yin watsi da bukatar tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawar, bisa wani rahoton hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS, da ke zargin Magu da aikata ba dai dai ba, wanda ta ce hakan yasa bai kamata ya shugabanci hukumar ta EFCC ba.

Daga cikin zarge zargen da jami'an tsaron farin kaya na DSS ke yiwa Magu akwai, zama a gidan da ake biyan kudin hayarsa kan Naira miliyan 20 a duk shekara, kuma ana biyan kudaden ne ba daga aljihun hukumar EFCC ba, inda hukumar DSS din ta ce wani babban jami’in gwamnati da ake bincika bisa aikata almundahana ke biyan kudin hayar.

To sai dai Ibrahim Magu ya musanta zargin, inda ko a Larabar da ta gabata, ya shaidawa zauren majalisar dattawan Najeriya cewa, har zuwa wannan lokaci, hukumar tsaron ta DSS bata gayyace domin kare kansa ba.

Har yanzu dai fadar gwamnatin Najeriya ba ta ce komai ba dangane da wannan lamari, bayanda a Larabar da ta gabata, bayan yin watsi da tabbatar da Magu a matsayin shugaban EFCC, shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki, ya bukaci fadar shugaban kasa ta gabatar da sunan wanda zai maye gurbinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.