Najeriya

Gwamnatin Najeriya za ta nazarci illar Fanta da Sprite

Ministan lafiya na Najeriya, Isaac Adewala da shugaba Muhammadu Buhari
Ministan lafiya na Najeriya, Isaac Adewala da shugaba Muhammadu Buhari guardian.ng

Gwamnatin Najeriya ta kira wani taron gaggawa don nazari kan illar da aka ce lemun kwalba na Fanta da Sprite ke yi wa dan Adam sakamakon wani hukuncin babbar kotu da ke jihar Legas.

Talla

Ministan kula da lafiya Issac Adewole ya bukaci hukumar NAFDAC da hukumar kula da ingancin kayan da ake sarrafawa ta Standard Organisation of Nigeria da su dauki matakan da suka dace kan lemun kwalbar don kare lafiyar 'yan kasar.

Ita dai kotun ta Legas ta bai wa kamfanin Coca Cola umurnin ya rubuta karara a jikin kwalbar Fanta da Sprite cewar, kada a sha lemun da Vitamin C domin yana da illa, sakamakon karar da wani dan kasuwa ya kai saboda sinadarin da kamfanin ke amfani da shi.

Shi dai wannan sinadari masana sun ce, yana haifar da cutar kansa da kuma daukewar numfashi idan an yi amfani da shi da yawa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.