Najeriya

Najeriya za ta hukunta masu hannu a rikicin Ile-Ife

Gwamnatin Najeriya za ta hukunta masu hannu a rikicin Ile-Ife da ya kashe mutane 46
Gwamnatin Najeriya za ta hukunta masu hannu a rikicin Ile-Ife da ya kashe mutane 46 citymirrornews

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar za ta hukunta duk wanda aka samu da hannu a tashin hankalin da akayi a garin Ile-Ife da ke Jihar Osun wanda ya hallaka mutane 46.

Talla

Ministan cikin gida Janar Abdurrahman Bello Dambazau ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci garin, bayan dawowarsa daga Afrika ta Kudu, in da aka kashe wasu 'yan Najeriya a rikicin kyamar baki.

A zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Janar Danbazau ya ce, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kafin daukan mataki kan duk wanda aka samu da hannu a rikicin tsakakin Hausawa da Yarbawa.

Danbazau ya ce, za a hukunta duk wanda aka samu da hannu kamar yadda dokata ta tanada.

Ministan tsaron ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Osun da masarautar Ife kan rawar da suka taka wajen magance rikicin.

Ministan ya kara da cewa, yanzu an samu zaman lafiya a garin kuma gwamnatin jihar ta kudiri aniyar gyara gidaje da shagunan al’ummar Hausawa da aka lalata sakamakon tashin hankalin.

 

 

Janar Abdurrahman Danbazau kan rikicin Ile-Ife

Akwai al'ummar Hausawa da dama da ke harkokin kasuwanci a jihar Osun da kuma wasu jihohin Yarbawa da ke kudancin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI