Najeriya

An garkame 'yan Najeriya 400 a Afrika ta Kudu

'Yan Afrika ta Kudu na kai wa baki 'yan cirani farmaki da suka hada da 'yan Najeriya
'Yan Afrika ta Kudu na kai wa baki 'yan cirani farmaki da suka hada da 'yan Najeriya ibtimes.co.uk

Mnistan cikin gidan Najeriya Janar Abdulrahman Danbazau mai ritaya, ya ce, kimanin ‘yan kasar 400 ne ke tsare a gidan yarin Afrika ta Kudu sakamakon aikata laifuka daban-daban. 

Talla

Danbazau ya sanar da haka ne bayan wata ziyara da tawagarsa ta kai Afrika ta Kudu don tattauana kan farmakin da ake kai wa baki a kasar da suka hada da ‘yan Najeriya.

A cewar Ministan, daga cikin wadanda aka garkame a gidan yarin, akwai wadanda ake zargi da karuwanci da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Danbazau ya kara da cewa, fursunonin za su kammala wa’adinsu na zaman kaso a Afrika ta Kudu saboda babu da wani shirin musayar fursunonin tsakanin kasashen biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.