Najeriya

NDLEA ta cafke mutane 34,499 kan ta'amali da kwayoyi a Najeriya

Hukumar hana sha da fataucin migayun kwayoyi a Najeriya, NDLEA, ta ce ta kama mutane sama da dubu 34 kan ta’anmali da miyagun kwayoyi a sassa daban daban na kasar daga 2012-2015.

NDLEA ta ce ta kama mutane sama da dubu 34 kan ta’anmali da miyagun kwayoyi a Najeriya
NDLEA ta ce ta kama mutane sama da dubu 34 kan ta’anmali da miyagun kwayoyi a Najeriya AFP/ Ernesto BENAVIDES
Talla

Rahotan da hukumar ta wallafa ya bayyana jihar Kano kan gaba da mutane 8,939 sai jihar Katsina a matsayin ta da mutane 2,173.

Hakazalika hukumar ta NDLEA ta bayyana cewa yanzu haka ta fara amfani da na’uorin gano miyagun kwayoyi a filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna, sakamakon yadda ake samun saukar jiragen ketara saboda rufe na Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI