Najeriya

Hamid Ali zai sake bayyana a gaban Majalisar dattawan Najeriya

Shugaban hukumar hana fasa kaurin kayayyaki ta Najeriya, Kwastam, Hamid Ali.
Shugaban hukumar hana fasa kaurin kayayyaki ta Najeriya, Kwastam, Hamid Ali. onlinenigeria.com

A gobe Laraba ake sa ran shugaban hukumar hana fasa-kauri wato Kwastam na Najeriya zai gurfana a gaban majalisar dattawan kasar.

Talla

Sai dai babban abinda ya fi daukar hankulan jama’a a kasar yayinda ake dakon wannan bayyana, shi ne yadda majalisar ta ce dole shugaban hukumar ta Kwastam Hamid Ali, ya sanya kaki kafin zaunawa da ‘yan majalisar.

A zantawar da yayi da sashin hausa na RFI, Alhaji Kiyari Abubakar Idris shugaban wata kungiyar fafutuka, na ganin cewa kamata ya yi a yi la’akari da muhimmancin aikin da shugaban hukumar ta Kwastam ke yi maimakon ci gaba da dagewa kan dole ya sanya kaki.

Idris ya zargi ‘yan majalisar da yunkurin ta yarwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari hankali, ganin cewa bai kamata a ce batun sanya kakin shugaban hukumar Kastam ya zama wani babban al’amari ba.

Zalika mai fafutukar ya ce tuni wasu masana shari’a da kundin tsarin mulkin Najeriya suka bayyana cewa bai zama wajibi shugaban hukumar ya sanya kaki ba, don kawai zai bayyana a gaban majalisar dattawan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.