Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya zata binciki Saraki da Dino Melaye

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki tare da Sanata Dino Melaye.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki tare da Sanata Dino Melaye. nigeriatoday.ng

Majalisar dattawan Najeriya, ta ce za ta binciki zargin da ake yi wa shugabanta Bokula Saraki, na yi wa motarsa mai sulke takardun kwastam na jabu.

Talla

Majalisar ta kuma ce, zata binciki wani dan majalisar, Dino Melaye da wasu ke cewa bai kammala karatun digirin da yake ikirarin yi a jami’ar Ahmadu Bello ba.

Matakin ya biyo bayan kudurin da sanata Ali Ndume, da ya ce, zarge zargen batanci ne ga majalisar dattawan a idon al’ummar Najeriya.

A zaman ta gudanar karkashin mataimakinta Ike Ekweremadu, majalisar dattawan ta mika batun binciken, ga kwamitinta na da’a, domin gudanar da bincike tare da gabatar da rahotonsa a cikin makwanni hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.