Najeriya

Lagos na cikin biranen duniya mafi arhar rayuwa

birnin Lagos tsohuwar fadar gwamnatin Najeriya
birnin Lagos tsohuwar fadar gwamnatin Najeriya REUTERS

Singapore shi ne birni mafi tsadar rayuwa a duniya, Hong Kong ne na biyu kamar yadda wani bincike da hukumar Economist Intelligence Unit ta gudanar. Almaty na Kazakhstan ne birni mafi saukin rayuwa a duniya, sai kuma birnin Lagos na Najeriya.

Talla

Biranen Japan guda biyu Tokyo da Osaka na cikin sahun birane 10 da suka fi tsadar rayuwa sakamakon darajar kudin yuan.

Birnin daya kacal a Amurka ke cikin jerin birane 10, kuma shi ne birnin New York wanda ke matsayi na 9, sai Los Angeles da ke matsayi na 11.

Birane 4 daga nahiyar Turai ke cikin jerin birane 10 kuma sun kunshi Zurich a matsayi na 3 sai Geneva da Paris wadanda ke matsayi na 7 sai kuma Copenhagen wanda ke kafada kafada da New York a matsayi na 9.

Birnin Almaty da ke Kazakhstan ne birni mafi saukin rayuwa a duniya, sai kuma birnin Lagos Najeriya.

Masu binciken sun yi la’akari da farashin kayan abinci da abin sha da sutira da kayan gida da kuma kayan sawa 160 wajen yanke hukunci.

A Singapore ana sayar da Biredi akan sama da Dala 3, sannan kwalbar giya sama da Dala 23, amma a Almaty Biredi Centi 90, yayin da giya ke Dala 10 da Centi 35.

Binciken ya ce biranen da ke tsaka-tsaki sun hada da Bangalore na India da Karachi da Pakistan da kuma birnin Algiers na Algeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.