Najeriya

Majalisar Najeriya ta bukaci tsige Hameed Ali

Shugaban hukumar Kwastam ta Najeriya Hameed Ali.
Shugaban hukumar Kwastam ta Najeriya Hameed Ali. onlinenigeria.com

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya sauke  Hameed Ibrahim Ali daga kujerar shugabancin hukumar hana fasa kauri ta kasar wato Kwastam. 

Talla

Majalisar ta ce, Hameed Ali bai cancaci rike wani mukamin jagorancin al'umma ba a kasar, yayin da  kuma ta bukaci hukumarsa ta Kwastam da ta soke shirinta na karban kudin fito na tsoffin motocin da aka shigo da su cikin kasar a can baya.

Wannan dambarwa dai ta yi kamari ne bayan shugaban Kwastam din ya yi watsi da gayyatar da Majalisar ta yi ma sa, in da ta bukace shi ya bayyana a gabanta sanye da kaki.

Har ila yau Majalisar Dattawan karkashin shugabanta, Sanata Bukola Saraki ta yi watsi da wasikar ministan shari’ar kasar Abubakar Malami da ke bukatar ‘yan majalisar da su janye kiran da suka yi wa Hameed Ali.

Da farko dai Majalisar ta ki sauraren Ali bayan ya bayyana a gabanta saboda rashin sanya kakin Kwastam kamar yadda ta bukace shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI