Bakonmu a Yau
Alhaji Kabir Kaita kan sa'insa tsakanin majalisar Najeriya da shugaban Kwastam
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:29
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban hukumar kwastam Hameed Ali ya sauka daga mukamin sa saboda abinda ta kira da rashin cika ka’idojin rike mukamin gwamnati. Majalisar wadda taki amincewa da wasikar da ministan shari’a na kasar Abubakar Malami ya rubuta mata dan jingine tattaunawa kan matsalar saboda maganar na gaban kotu, ta bayyana damuwar ta kan rashin amsa gayyatar shugaban na kwastam. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tuntubi, Alhaji Kabir Babba Kaita tsohon babban jami’i a hukumar ta kwastam, wanda yayi mana tsokaci akai.