Najeriya

Hukumar tsaron Najeriya ta sake kame kwamandan boko haram

Hukumar tsaron farin kayan Najeriya DSS, ta sanar da sake kama wani kwamandan kungiyar boko haram, Nasiru Sani, da ya tsere daga gidan yarin Bauchi a shekarar 2010.

Operatives of the Department of State Services (DSS), Nigeria.
Operatives of the Department of State Services (DSS), Nigeria. guardian.ng
Talla

Kakakin hukumar Tony Opuiyo, yace jami’an hukumar sun kuma kama wani Adamu Jibrin a Jeka da fari dake Gombe, wanda ya amsa cewar yana cikin kungiyar ta boko haram.

Opuiyo ya kuma bayyana cewa hukumar ta kame wasu jiga jigan kungiyar ta Boko Haram a samamen da jami’anta suka kai a sassan kasar da suka hada da
Bauchi, Kano, Kaduna, Kogi da kuma Yobe.

Hukumar ta ce daga cikin wadanda aka kama a samamen akwai wani matashi mai shekaru 29, Usman Ladan Rawa da aka damke a garin Lafiya, jihar Nasarawa, a ranar 17 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI