Najeriya

Rundunar Najeriya ta rusa masana'antar bam ta Boko Haram

Sojin Najeriya na ci gaba da kakkabe sauran mayakan Boko Haram a maboyarsu
Sojin Najeriya na ci gaba da kakkabe sauran mayakan Boko Haram a maboyarsu © Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta lalata masana’antar kera bama-bamai ta kungiyar Boko Haram da ke kauyen Gombole a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno. 

Talla

Wata sanarwa da mai mgana da yawun rundur sojin kasar Birgediya Janar Sani Usman ya fitar ta ce, dakarun batalitya ta 103 na Operation Lafiya Dole ne suka gano masana'antar a yayin gudanar da aikin tsaftace kauyen Gombole.

Usman ya kara da cewa, dakarun sun kuma yi nasarar ceto mata hudu da kananan yara shida da Boko Haram ta yi garkuwa da su.

Hr ila yau, sojojin sun samu rigunan bama-bamai guda hudu da Babura da kuma kakin soji da kungiyar ta sace.

Tun bayan fatattakar mayakan Boko Haram daga dajin Sambisa da ya kasance babbar matattararsu, sojojin Najeriya ke ci gaba da shiga lungu da sako na jihar Borno da nufin gano ‘yan ta’addan da suka buya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI