Najeriya

'Yan Kungiyar Boko Haram da aka Tarwatsa daga Dajin Sambisa na ta farautar Abinci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Cameroon Paul Biya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Cameroon Paul Biya AFP PHOTO / REINNIER KAZE

An gano cewa akwai fargaba da zaman dar-dar a jihar Borno sakamako yadda ‘yan kungiyar Boko Haram, da ake ta fatattaka daga kauyuka ke bazama neman abinci da magunguna ta kowani hali.

Talla

Majiyoyin samun labarai sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, a irin wannan farautar abinci da magunguna, mayakan kungiyar ta Boko Haram dake biyayya ga Abu Musab Al-Barnawi sun kai wani hari Sabon Garin Kimba mai nisan kilomita 140 daga Maiduguri inda basu kashe kowa ba saidai kwace kayan abinci.

A cewar kafofin samun labarai ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun shiga garin ne cikin jerin gwanon motoci a kori kura.

Fararen hula dake taimakawa soja murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram sun shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransan, AFP,  cewa bisa dukkan alamu taron dangi da aka yiwa ‘yan Boko Haram ya karya lagon su.

Littini din nan ake sa ran tawaga ta musamman daga Gwamnatin Tarayyar Najeriya zuwa dajin Sambisa, makwancin Boko Haram da aka tarwatsa su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.