Najeriya

CBN ya karya darajar dala

CBN ya karya darajar dala
CBN ya karya darajar dala REUTERS

Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan kasar da nan take su fara sayar da dalar Amurka ga kwastomominsu kan naira 360.

Talla

A cewar bankin na CBN, za’a soma sayarwa bankunan dala kan naira 357, dan haka ya bukaci nan take, su sanar da dukkanin rassansu da ke sassan kasar, dangane da sabon sauyin.

A yau litinin bankin ya wallafa daukar matakin da baya rasa nasaba da yunkurin rage gibin da ke tsakaninta da ta kasuwanin bayan fage.

Faduwar darajar naira a Najeriya ta haifar da matsalar hauhawar farashin kayayyaki a kasar al’amarin da ya kara jefa al’umma cikin kuncin rayuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.