Najeriya

Majalisar Najeriya ta bijirewa Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke gabatarwa Majalisa kasafin kudin 2017
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke gabatarwa Majalisa kasafin kudin 2017 REUTERS/Stringer

Majalisar Dattawan Najeriya ta jingine tantance kwamishinonin Hukumar zaben kasar 27 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata saboda abinda suka kira kin korar shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Talla

Majalisar ta kuma zargi wasu daga cikin jami’an Gwamnati Buhari da rashin yi musu da’a wajen gudanar da ayyukan su.

Sau biyu Majalisar ta na watsi da Magu a matsayin shugaban Hukumar da ke yaki da cin hanci da Rashawa EFCC.

Majalisar na kuma takun-saka da Shugaban Hukumar kwastam ta kasa Hameed Ali da kuma sakataren gwamnati Babachir Lawan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI