Najeriya

Majalisar Najeriya ta dakatar da Ndume

Sanata Ali Ndume
Sanata Ali Ndume

Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar, Sanata Ali Ndume har na tsawon watanni shida. 

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Ndume ya bukaci a gudanar da bincike game da zargin cewa, an yi amfani da takardun bogi wajen shigo wa shugaban Majalisar Sanata Bukola Saraki da mota mai silke kirar Range Rover.

Kazali Mr. Ndume ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan zargin Dino Melaye game da ingancin takardun shedar kammala karatunsa na Jami’a.

Majalisar ta dakatar da Ndume ne bayan ya bayyana a gaban Kwamitin da’a da ya gudanar da zaman sauraron shi kan kalamansa na cewa, Saraki na daukan matan ramako ne kan shugaban hukumar Kwastam Hamid Ali mai ritaya da ke takun saka da Majalisar saboda rashin sanya kaki a matsayinsa na shugaban Kwastam.

Har ila yau Majalisar ta wanke Saraki da Melaye kan zarge-zargen da ake yi musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.