Bakonmu a Yau

Barrister Ahmed Goniri: Hukuncin daurin rai da rai kan mai aikata fyade

Wallafawa ranar:

Gwamnatin Jihar Yobe dake Najeriya na shirin aiwatar da wata dokar daurin rai da rai ga wadanda aka samu da laifin aikata fyade, sakamakon karuwar aikata laifin da aka samu a sassan jihar. Gwamnatin ta bukaci goyan bayan Majalisa wajen ganin an aiwatar da dokar domin dakile yaduwar aikata laifin. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris, ya tattauna da Barrister Ahmed Goniri, kwamishinan shari’a na jihar.  

Babbar Kotu a Najeriya.
Babbar Kotu a Najeriya. nigerianpilot.com
Sauran kashi-kashi