Najeriya

Buhari zai koma London don ganin likitocinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari SEYLLOU / AFP

Fadar gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa, shugaban kasar Muhammdu Buhari zai gayyato likitocinsa na London don duba lafiyarsa a gida a maimakon komawa Ingila.

Talla

Mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya ce, babu gaskiya a cikin rahotannin da aka yi ta yadawa musamman a shafukan sada zumunta da ke cewa Buhari ba zai koma London ba.

Sai dai kakakin na Buhari ya sanar da ranar da shugaban zai koma London din ba.

Bayan dawowarsa gida makwanni uku da suka gabata, shugaba Buhari ya ce zai koma birnin London nan da wani lokaci don sake ganin likitocinsa.

Buhari dai ya shafe kwanaki 49 yana jinya a can London, abin da ya haifar da cece-kucen a fadin Najeriya, in da wasu ke ta rade-radin cewa shugaban ya rasu.

Kazalika shugaba Buhari ya ce, bai taba jinya ba a rayuwarsa da ta kai wacce ya yi a London din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.