Najeriya

Ana jayayya kan kudaden da EFCC ta kama a Legas

Ibrahim Magu
Ibrahim Magu

Wata bbabar kotun tarayya da ke jihar Legas ta Najeriya, ta bai wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar wato EFCC izinin adana makuden kudaden da ta gano a unguwar Ikoyi da ke Legas. 

Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da cecekuce dangane da ainihin mamallakin kudaden da yawansu ya zarce Naira Biliyan 10.

Ana rade-radin cewa, hukumar leken asirin kasar da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike , kowanne daga cikinsu na ikirarin cewa, mallakashinshi ne.

An gano kudadden ne a yayin da hukumar ta kai samame a wani gida da aka ce na tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne Ahmad Ma'azu a ranar Laraba, amma daga bisa ya shaida wa manema labarai cewa, tuni ya siyar da gidan na Ikoyi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da hukumar ke kai samame tare da kwato makuddan kudade ba daga hannun wadanda ake zargi da halasta kudaden haramun.

A yayin gudanar da bikin cika shekaru 14 da kafuwar EFCC a makon jiya, mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu ya bayyana cewa, za su ci gaba da yaki da masu yi wa tattalin arzkin Najeriya ta’annati don kawar da cin hanci baki daya, abin da ya ce, zai dawo da martabar kasar a idon duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.