Bakonmu a Yau

DR Isa Fantami: Samar da ayyukanyi ta hanyar fasahar sadarwa a Najeriya

Sauti 03:37
Newly appointed Director-General of the National Information Technology Development Agency (NITDA) of Nigeria, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.
Newly appointed Director-General of the National Information Technology Development Agency (NITDA) of Nigeria, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami. iittelecomdgest.com

Hukumomin Najeriya sun ce fasahar zamani zata samar da ayyukan yi sama da miliyan 3 da kuma kudaden shiga ga kasar da yawansu ya kai Dala biliyan 88 nan da shekaru 10 masu zuwa. Ministan kasuwancin Najeriya Dr Okechukwu Enelamah, ya bayyana haka a wajen wani taron ministocin kasashe masu tasowa da ake gudanarwa a birnin Geneva karkashin Majalisar Dinkin Duniya. Enelamah yace Najeriya na da dimbin matasan da suka yi fice a fannin kere kere da sadarwa wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. Yayin zantawarsa da Bashir Ibrahim Idris na sashin hausa na RFI, Dr Isa Ali fantami, Darakta Janar na Hukumar NITDA dake kula da fasahar ta zamani a Najeriya ya ce lokaci ne yayi da Najeriya zata kauracewa dogaro da man fetur domin karfafa tattalin arzikinta, idan aka yi la’akari da halin da kasar ta fada na matsi sakamakon dogaro kan abu daya.