Najeriya

Dan Majalisar wakilai ya tsallake rijiya da baya a Najeriya

Dan Majalisar wakilan Najeriya ya tsallake rijiya da baya
Dan Majalisar wakilan Najeriya ya tsallake rijiya da baya

Wani Dan Majalisar wakilan Najeriya daga Jihar Kano, Garba Durbunde, ya tsallake rijiya da baya, sakamakon kama shi da masu garkuwa da mutane suka yi akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Talla

Rahotanni sun ce, wasu daga cikin abokan aikin sa daga Yankin Arewa maso gabas suka biya diyyar naira miliyan 6 kafin a sako shi.

Garkuwa da mutane dan karbar kudi na kokarin sama ruwan dare a Najeriya.

Yanzu haka a Jihar Lagos, 'Yan Sanda na farautar wasu da suka sace daliban wata makaranta, kuma suka bukaci biyan su diyyar naira miliyan 400.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.