Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Jami'o'i 38 sun kara kudin karatu

Wasu daliban jami'a a harabar Jami'ar UNILAG da ke birnin Legas
Wasu daliban jami'a a harabar Jami'ar UNILAG da ke birnin Legas homelandnewsng
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 3

Akalla Jami’o’in Najeriya 38 ne suka kara wa dalibai kudaden makaranta, matakin da suka danganta da rashin samun isassun kudade daga gwamnatocin tarayya da kuma na jihihohi.

Talla

Jami’oin da suka kara kudaden sun hada da ta Ahmadu Bello da ke Zaria, da ta yi karin kudin daga 27,000 zuwa 41,000, yayinda Jami’ar Bayero a Kano, ta yi karin kudin ne daga 26,000 zuwa 40,000.

Jami’ar babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, ta yi nata karin ne daga 39,300 zuwa 42,300.

Sai Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto, da ta kara 32,000 zuwa 41,000, yayinda da kuma Jami’ar Obafemi Awolowo ta kara naira 19,700 zuwa 55,700.

A lokacin da yake tsokaci kan matakin karin kudin, Dr Ahmad Galadima Malami a Jami’ar Gusau ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewa, dole ke sa ake kara kudaden ga dalibai domin gudanar da wasu muhimman ayyukan tafiyar da jami’oin.

Galadima ya ce cigaba da karuwar yawan dalibai a jami’o’in, na daya daga cikin dalilan da suke tilasta yin karin kudin makarantar, saboda rashin isassun kudade daga gwamnati.

Galadima: Najeriya: Jami'o'i 38 sun kara kudin karatu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.