Najeriya

Dattawan kabilar Igbo sun yi watsi da fafutukar kafa kasar Biafra

Wasu da ke fafutukar neman kafa kasar Biafra a garin Aba da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Wasu da ke fafutukar neman kafa kasar Biafra a garin Aba da ke kudu maso gabashin Najeriya. STEFAN HEUNIS / AFP

Shugabannin yankin kudu maso gabashin Najeriya, sun yi watsi da kiraye-kirayen ballewar yankin domin kafa kasar Biafra, wanda kungiyoyin IPOB da MASSOB ke yi.

Talla

Taron ya samu halartar ilahirin gwamnonin jihohin yankin, da ‘yan majalisu yankin, sai kuma dattawan kabilar Igbo wato Ohaneze, a garin Enugu.

Dattawan sun ce suna goyon cigaba da zaman Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa, sai dai akwai bukatar a dauki matakin sake fasalta tsarin tafiyar da al’amuran kasar.

Takardar bayan taron da shugabannin yankin na kudu maso gabashin Najeriya suka sa wa hannu, ta bukaci gwamnatin kasar ta soma aiwatar da matakan da ake bukata don sake fasalta tsarin tafiyar da harkokin gwamnati.

Zalika sun kuma bukaci da fara aiwatar da kudurorin taron da aka cimma a taron tattauna matsalolin kasa da ya gudana a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.