Najeriya

Najeriya: Sama da mayakan Boko Haram 700 zasu mika kansu

Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Lafatanar Janar Tukur Yusuf Buratai.
Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Lafatanar Janar Tukur Yusuf Buratai. thenewsnigeria

Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Lafatanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya ce sama da mayakan Boko Haram 700 zasu mika makamansu ga rundunar musamman ta “Operation Lafiya Dole” da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.

Talla

Kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Sani Usman ya ce samun nasarar ya biyo bayan kara kaimin da suka yi wajen ruwan bama-bamai kan maboyar mayakan na Boko Haram babu kakkautawa, musamman a ranar 3 ga watan Yulin da muke ciki.

Yayin da yake tattaunawa da sashin hausa na RFI, kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Sani Usman, ya ce tuni 70 da ga cikin mayakan suka mika kansu.

Zalika daga cikin mayakan 700, akwai manyan masu fada a ji a cikin kungiyar ta Boko Haram.

Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka/ Sama da mayakan Boko Haram 700 zasu mika kai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.