Najeriya
Hukumar EFFC ta cafke Saminu Turaki
Wallafawa ranar:
Wasu bayanai na cewa jami’an hukumar yaki da rashawa EFCC a Najeriya sun cafke tsohon gwmanan jihar Jigawa Ibrahin Saminu Turaki, wanda hukumar ta jima tana kalubalantar sa a gaban kotu dangane da handame dukiyar jihar Jigawa.
Talla
Bayanai dai na nuni da cewa hukumar ta EFCC ta jima tana neman tsohon gwmanan domin gurfanar da shi a gaban kotu, to amma an kasa samunsa duk da cewa an sallame shi ne a karkashin beli.
Ibrahim Saminu Saraki ya kasance Gwamnan jihar ta Jigawa a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu