Najeriya-Kamaru

Bakassi: Najeriya ta bukaci bayani daga Kamaru kan kisan 'ya'yanta

Wasu daga cikin mazauna yankin Bakassi
Wasu daga cikin mazauna yankin Bakassi dailypost.ng

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta bukaci jakadan Kamaru da ke kasar, Abbas Salahedine, ya yi Karin haske, kan rahoton cin zarafi hadi da kisan gillar da Jardarmomin kasar ta Kamaru suka yi wa wasu ‘yan Najeriya mazauna yankin Bakassi.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta bayyana bacin ranta bisa cin zalin da aka yiwa fararen hular, wanda ta ce ya auku ne, sakamakon gaza biyan haraji da ‘yan Najeriyar suka yi, bisa sana’ar SU da suke yi a yankin na Bakassi.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai, rahotanni suka bulla cewar, Jandarmomin Kamaru sun hallaka akalla ‘yan Najeriya 97 mazauna yankin na Bakassi, saboda sun gaza biyawa kanan jiragen ruwan da suke amfani da su wajen sana’ar SU haraji, na kwatankwacin naira dubu dari.

Tuni ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta Umarci ofisohinta da ke Yaounde da Buea su gudanar da bincike kan al’amarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.