Najeriya

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta musanta rahoton tserewar Evans

Kasurgumin mai sata da garkuwa da mutane a Najeriya, da ya shiga hannun jami'an tsaro, Chukwudumeje George Onwuamadike, da ke amsa sunan Evans.
Kasurgumin mai sata da garkuwa da mutane a Najeriya, da ya shiga hannun jami'an tsaro, Chukwudumeje George Onwuamadike, da ke amsa sunan Evans. gistsvilla.com

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta karyata rahotannin da ke cewa kasurgumin mai sata da garkuwa da mutane, mai amsa sunan Evans, da ta kame a birnin Legas, ya tsere daga hannunta.

Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jimoh Moshood ya ce babu gaskiya a cikin rahoton da wata jaridar kasar ta wallafa, na cewa Evans ya sulale daga hannunsu.

A cewarsa Evans din yana cigaba da basu hadin kai, da ya basu nasarar kamu Karin na hannun damansa da suke dade suna tafka ta’asar sata da garkuwa da mutane har ma da fashi.

Tun a ranar 10 ga watan Yunin da ya gabata wata tawagar rundunar ‘yan sandan Najeriya, karkashin jagorancin Abba Kyari, ta samu nasarar kame Evans a gidansa da ke birnin Legas, bayan shafe akalla shekaru 7 tana farautarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.