Kungiyar Miyatti Allah zata garzaya Kotun Duniya
Wallafawa ranar:
Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah a Najeriya, tace ta sanya lauyoyinta tattara alkaluman baranar da aka yi mata, dan ganin sun gabatar da kara a kotun duniya bayanda aka yi wa ‘ya’yanta kisan gilla a jihar Taraba.
Kungiyar ta kuma bukaci Gwamnatin Najeriya da ta kafa kwamitin bincike na musamman domin bi mata hakkin rayuka da kuma dukiyar Fulani da aka salwantar.
Yayinda yake zantawa da Bashir Ibrahim Idris na RFI Hausa, Alhaji Baba Usman Ngelzerma, Sakataren kungiyar na kasa yace dukkanin matakan da zasu dauka don bin hakkinsu, zasu bi doka da oda ne.
A cewar Alhaji Baba, basu gamsu da binciken da gwamnatin jihar Taraba ta gudanar ba kan kisan gillar da aka yi wa Fulani a makwannin da suka gabata, dan haka ne ma ya zama tilas su garzaya kotun duniya, domin neman a yi musu adalci.
Kungiyar Miyatti Allah zata garzaya Kotun Duniya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu