Bakonmu a Yau

Kungiyar Miyatti Allah zata garzaya Kotun Duniya bisa kisan da aka yi wa 'ya'yanta a Taraba

Sauti 03:18
Fulani makiyaya
Fulani makiyaya guardian.ng

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah a Najeriya, tace ta sanya lauyoyinta tattara alkaluman baranar da aka yi mata, dan ganin sun gabatar da kara a kotun duniya bayanda aka yi wa ‘ya’yanta kisan gilla a jihar Taraba. Kungiyar ta kuma bukaci Gwamnatin Najeriya da ta kafa kwamitin bincike na musamman domin bi mata hakkin rayuka da kuma dukiyar Fulani da aka salwantar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Baba Usman Ngelzerma, Sakataren kungiyar Miyatti Allah na kasa.