Ilimi Hasken Rayuwa

Matashi dan Najeriya ya shahara wajen kere-kere

Wallafawa ranar:

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, wanda Bashir Ibrahim Idris ke gabatarwa, yayi tattaki ne zuwa jihar Filato, inda ya tattauna da wani matashi Jerri Isaac Malo, wanda Allah ya bai wa fashar kere-kere. Bayan kawo muku takaitaccen tarihin matashin, shirin ya kuma yi nazari kan ire-iren kere-keren da matashin ya samu nasarar yi, lamarin da ya daga darajarsa a idon al'ummah.

Motar tantan ta noma da matashi Jerry Isaac dan jihar Filato ya kera a Najeriya.
Motar tantan ta noma da matashi Jerry Isaac dan jihar Filato ya kera a Najeriya. RFI Hausa/Bashir Ibrahim Idris