Najeriya

Osinbajo ya ziyarci Buhari a birnin London

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.
Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. citypeopleonline

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osibanjo ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a birnin London, in da yake jinyar rashin lafiyar da ya ke fama da ita.

Talla

Kakakin mukaddashin shugaban Laolu Akande, ya ce bayan kammala ganawar shugabannin biyu, Farfesa Osibanjo zai koma gida a daren yau domin ci gaba da gudanar da ayyukansa.

Shugaba Buhari ya kwashe kwanaki 64 a birnin London, in da ake kula da lafiyarsa, sai dai kafin barin kasar ya aike da takarda zuwa Majalisa wadda ta tabbatar da mika wa mataimakinsa karagar mulki.

Ya zuwa yanzu dai, babu cikakken bayani kan dalilin ziyarar da kuma batutuwan da za su tattauna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.