Najeriya

''Buhari na Murmurewa yana dab da dawo wa''

Mukaddashin Shugaban kasar Najeriya Ferfesa Yemi Osinbajo
Mukaddashin Shugaban kasar Najeriya Ferfesa Yemi Osinbajo citypeopleonline

Mukaddashin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce, shugaban kasar, Muhammadu Buhari da ke jinya a birnin London na murmurewa cikin gaggawa kuma nan gaba kadan zai koma gida don ci gaba da jagorancin kasar.

Talla

Osinbajo da ya kai wa Shugaba Buhari ziyarar kwana guda, ya ce sun yi kyakyawar ganawa ta sa’a guda a kan batutuwa da dama, kuma shugaban na murmurewa cikin gaggawa da yanayi mai kyau.

Sai dai Osinbajo bai bayyana ainihi batutuwan da ya tattauna da Buhari a ziyarar da ya kai masa jiya talata ba.

‘Yan adawa na ci gaba da cewa, ya dace a bayyana wa ‘yan Najeriya hakikanin rashin lafiyar da ke damun Buhari don sanin makomarsa a kan karaga.

Sama da watanni biyu kenan da shugaba Buhari ya shafe yana jinya a birnin London yayin da 'yan kasar ke dakon ranar dawowarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI