Najeriya

Ambaliyar ruwa za ta iya shafar jihohi 30 a Najeriya

Ambaliyar ruwa za ta iya shafar jihohi 30 da kananan hukumomi sama da 100 a Najeriya a cikin wannan shekarar
Ambaliyar ruwa za ta iya shafar jihohi 30 da kananan hukumomi sama da 100 a Najeriya a cikin wannan shekarar Louisiana Department of Transportation and Development/Handout

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gargadi samun ibtila’in ambaliyar ruwa a jihohi 30 da kuma kananan hukumomi 100 da ke sassan kasar, sakamakon ruwan sama da ake tafkawa kamar da bakin-kwarya a cikin wannan shekarar.

Talla

Gwamnatin ta yi gargadin ne a yayin da Ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu ke jajanta wa wadanda ambaliyar ta sha a ‘yan kwanakin nan.

Ministan ya bada tabbacin cewa, hukumomin kasar za su ci gaba da sanya ido dangane da tinkarar ambaliyar ruwan, yayin da ya ce, ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen fitar da sanarwa akai-akai.

Har ila yau, Ministan ya shaida wa ‘yan Najeriya cewa, nan gaba kadan, za a samar da manyan dam-dam na ruwa a fadin kasar don magance matsalar ambaliyar da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

A bangare guda, gwamnatin kasar ta shawarci mazauna birane da su guje wa gine-gine a magudanan ruwa.

Tuni dai mukaddashin shugaban Najeriya, FarfesaYemi Osinbajo ya bada umarnin sakin Naira biliyan dubu 1 da miliyan 600 ga jihohi 16 da ambaliyar ta shafa a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.