Najeriya

Najeriya: Gwamnati ta yanke shawara kan matsayin matatun mai

Gwamnatin tarayyar Najeriya, majalisar dattijan kasar da kuma masu ruwa da tsaki a harkar man fetur sun cimma matsayar karbo bashi don gyara matatun man kasar da su maimakon bayar da jinginar su ga kamfanoni masu zaman kan su.

Matatar man Najeriya da ke garin Fatakwal
Matatar man Najeriya da ke garin Fatakwal eeenergy.ng
Talla

An dai cimma wanna matsaya ce bayan sauraron ra’ayoyin jama’a, da majalisar Dattijan ta shirya a kan batun na yunkurin farfado da matatun man.

A baya ma dai batun jinginar da matatun man a Najeriyar ya haddasa cece-kuce tsakanin al’ummar kasar.

Sai dai ministan albarkatun man Najeriya Dr Ibe Kachikwu ya musanta cewa gwamnati a baya ta yi shirin jinginarwa ko kuma sayar da matatun man kasar ga wasu kamfanonin kasashen ketare.

Dangane da shawarar farfado da ayyukan matatun man kuwa, Kachikwu yayi Karin bayanin cewa, a yanzu haka gwamnatin Najeriya na bukatar akalla dala miliya 300 domin farfado da ilahirin matatun man kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI