Bakonmu a Yau

Najeriya: Gwamnati ta yanke shawara kan matsayin matatun mai

Sauti 03:20
Matatar man Najeriya da ke garin Fatakwal
Matatar man Najeriya da ke garin Fatakwal eeenergy.ng

Gwamnatin tarayyar Najeriya da majalisar dattijan kasar da kuma masu ruwa da tsaki a harkar man fetur sun cimma matsayar karbo bashi don gyara matatun man kasar da su maimakon bayar da jinginar su ga kamfanoni masu zaman kan su. An dai cimma wanna matsaya ce bayan sauraron ra’ayoyin jama’a, da majalisar Dattijan ta shirya a kan batun na yunkurin farfado da matatun man. A baya ma dai batun jinginar da matatun man a Najeriyar ya haddasa cece-kuce tsakanin al’ummar kasar. Kan haka ne Azima Bashir Aminu, ta tattauna da Injiniya Khailani Muhammad, masani kan harkokin man fetur kuma tsohon shugaban matatar mai ta Kaduna a tarayyar Najeriyar.