Najeriya

Najeriya: An kashe triliyan 7 kan sayo kayan da aka sarrafa a ketare

Ministar kula da bunkasa masan’antu, zuba hannun jari da kuma ciniki ta Najeriya, Aisha Abubakar
Ministar kula da bunkasa masan’antu, zuba hannun jari da kuma ciniki ta Najeriya, Aisha Abubakar realnewsmagazine

Ministar kula da bunkasa masan’antu, zuba hannun jari da kuma cinikayya ta Najeriya, Aisha Abubakar, ta ce a shekara ta 2015 da ta gabata kadai, akalla naira triliyan 7 aka kashe domin shigo da kayan masaufi, da sauran kayayyakin da aka sarrafa a kasashen ketare zuwa cikin kasar.

Talla

Ministar ta bayyana  alkallumman ne yayin da ta ke jawabi a zauren taron da masu ruwa da tsaki kan kasuwanci suka shirya a jihar Kano, don kokarin sauya ra’ayin ‘yan Najeriya daga fifita kayan da aka sarrafa a kasashe ketare zuwa ga na gida.

A cewar Aisha, da ace an kashe wadannan makudan kudaden kan bunkasa kananan masana'antu na cikin gida, da kuma tallafawa masu sana'ar hannu, da tuni Najeriya ta dade da samun cigaba wajen fara kokarin dogaro da kanta, wajen sarrafa kayayyaki kirar gida.

Kiddigar ta ce daga cikin yankin makudan kudaden da aka kashe akwai, triliyan 1 da miliyan 9, wajen shigo da kayan abinci da sha cikin Najeriya daga ketare, yayinda aka kashe tiriliyan 1 da rabi, domin shigo da kayan gyaran ababen hawa, sai kuma naira biliyan 123 da aka kashe wajen shigo da talkalman da aka sarrafa su a ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI