Najeriya-Boko Haram

Borno: Wani yaro ya rasa ransa bayan daura masa damarar bam

Wata damarar Bam da aka cire daga jikin wani yaro mai shekaru 12 da yayi yunkurin kutsawa zuwa cikin jami'ar jihar Maiduguri, a makwannin da suka gabata.
Wata damarar Bam da aka cire daga jikin wani yaro mai shekaru 12 da yayi yunkurin kutsawa zuwa cikin jami'ar jihar Maiduguri, a makwannin da suka gabata. Musiclow

Wani yaro mai shekaru 10 ya rasa ransa a jihar Borno, da ke arewa maso gabashin Najeriya, bayan tarwatsewar damarar bam din da mayakan Boko haram suka daura masa.

Talla

Lamarin ya auku ne a jiya asabar kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sanda jihar DSP Victor Isuku ya tabbatar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, da misalin karfe 10 na safiyar jiya Asabar, wasu yara Fulani biyu Gambo Bukar mai shekaru 10 da kuma Umar bukar mai shekaru 8, daga kauyen Dalti da ke karamar hukumar Jere, suka fita kiwo, a nan ne suka gamu da wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, wadanda suka daura musu damarar bama baman, kafin sakinsu.

Rahoton ya kara da cewa, bayan dawowar yaran gida babu wanda ya bayyana abinda ya faru, wanda kuma garin cire damarar da aka daura musu, tarwatsewar bam din ya hallaka Gambo Bukar, yayinda shi kuma Umar aka garzaya da shi zuwa asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.